Sai dai matakin zai dada harzuka Haramtaciyar kasar Isra’ila kamar yadda ta faru bayan majalisun kasashen Birtaniya da Sweden suka yi a baya.
Tuni Faransa ta bayyana cewa idan lokaci ya yi za ta amince da kasar Falasdinu domin kawo karshen rikicin gabas ta tsakiya.
Ministan harakokin wajen Faransa Laurent Fabius ya shaidawa Kwamitin sulhu cewa Faransa a shirye ta ke ta jagoranci tattaunawar sulhu tsakanin Isra’ila da Falasdinawa.
A cewarsa samun ‘yancin Falasdinawa it ace hanyar warware rikicin gabas ta tsakiya.
Amma Firaministan Haramtaciyar kasar Isra’ila ya gargadi Faransa da cewa amincewa da kudirin babban kunskure ne.ABNA